Faransa ta haramta karuwanci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An yi kiyasin cewar akwai karuwai tsakanin 30,000 da 40,000 a Faransa

Majalisar dokokin kasar Faransa ta zartar da wata sabuwar dokar da ta hana biyan karuwai kudi domin yin lalata da su.

A dokar, a karo na farko za a ci tarar duk mutumin da aka kama ya biya karuwa kudi domin ya sadu da ita dala 1700 .

An yi kiyasin dokar dai, zata shafi karuwai kimanin 30,000, wadanda akasarinsu 'yan kasashen waje ne.

Maud Oliver, wanda shi ne kan gaba wajen samar da dokar, ya ce dole ne a sauya tunanin mutane na cewar ba wani abu ba ne don an biya karuwa kudi domin a yi lalata da ita.

Wata kungiyar karuwai da basu da yawa, masu dauke da kyallaye da aka rubuta "kar ku 'yanta ni, zan kula da kaina!" sun yi zanga-zanga a harabar majalisar Faransan don nuna adawa da dokar.