Kungiyar 'yan uwa Musulmi za ta gana da El-Zakzaky

Image caption Kungiyar ta shi'a ta bukaci a saki shugaban nata Sheikh Alzakzaky.

A Nigeria, gwamnati ta bai wa kungiyar 'yan uwa muslmi ta Islamic Movement in Nigeria IMN, damar ganawa da Sheikh El-Zakzaky, shugaban Shi'a na kasar.

Wannan damar ta biyo bayan kin amincewa da kungiyar ta yi na shiga tattaunawar da gwamnatin ta shirya tsakaninta da hukumar gudanar da shari'a, idan har ba a bai wa Sheikh Al-Zakzakin damar tofa albarkacin bakinsa ba.

Mutane hudu ne aka shirya ganawarsu da Alzakzaky, wadanda suka hada da lauyoyi uku da kuma mamba daya na kungiyar ta IMN.

Cikin lauyoyin har da Mista Femi Falana, hamshakin lauyan nan mai kare hakkin bil adama, da Barista Maxwell Nkiyom da Barista Kabir Muhammad, da kuma Sheikh AbdulRahman Abubakar, wanda dan kungiyar ne ta IMN.

Rahotanni dai sun ce shugaban 'yan shi'an na nan yana jinya a asibitin sojoji, tare da mai dakinsa Zeenat Ibrahim, bayan dirar mikiyar da sojojin kasar suka yi masa a gidansa da ke Zaria a watan Disambar da ya gabata.

Ana kyautata zaton wannan ganawar zai iya kawo maslaha ga dangantakar da ta yi tsami tsakanin gwamnatin kasar da mabiya shi'a da ke kasar.