IS: An kama dan Najeriya a Munich

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan sanda a Munich sun tsaurara tsaro a birnin, duba ga yadda kungiyoyin ta'adda ke ci gaba da kai hari a kasashen Turai.

'Yan sanda a Bavaria sun ce sun kama maza biyu, daya dan Iraki daya kuma dan Najeriya, bisa zargin su da kulla wani babban abu na neman tayar da fitina.

Jami'an sun ce an tsare dan Irakin mai shekaru 46 tare da dan Najeriyan mai shekaru 29 a ofishin 'yan sanda a Munich, ranar Alhamis ne, bayan an tsegunta wa jami'an tsaron game da mutanen.

Koda yake ba a bayar da karin bayani ba, amma Sueddeutsche Zeitung da ke Munich ta ce mai shigar da kara a birnin Thomas Steinkraus Zeitung ya ce akwai alamu da ke nuna mutanen biyu na da alaka da kungiyar dake ikirarin kafa daular musulinci, watau IS.

'Yan sanda dai sun ce ba a ga wasu muggan makamai tare da su ba, kazalika babu alamun cewa akwai wata barazana ga al'umma.