Iraki: Yunwa na gallabar mazauna Fallufa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Al'ummar Iraki na yawan fuskantar hare-hare
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce mazauna birnin Fallufa na kasar Iraki da aka yiwa kawanya na fama da azabar yunwa.

Dakarun gwamnati sun datse hanyar kai kayayyaki zuwa birnin, wanda suke kokarin sake kwacewa daga hannun mayakan IS.

Kungiyar wadda ke New York ta ce abinci kadan ne yanzu ake da shi a birnin don haka mutane na cikin matsananciyar yunwa.

Wakilin BBC ya ce lamarin ya yi kamari inda har mutane sun koma shan miyar da aka yi da ciyawa.

Akwai rahotannin da ba'a tabbatar da su ba na mace-mace sakamakon rashin abinci da magunguna.