Kotu ta yi hukunci akan gidan Mandela

Wata kotun Afirka ta kudu ta yanke cewa, tsohuwar matar marigayi Mandela, wato Winnie Madikizela-Mandela ba ta da hakki a gidansa na ƙauye.

Marigayi Nelson Mandela ya saki Winnie a shekarar 1996 bayan sun auren kusan shekaru 40.

Kuma marigayi Mandela bai saka tsohuwar matar tasa cikin wasiyyar da ya bari ba.

Ita dai Winnie Mandela ta dage cewa, bisa al'ada gidan marigayi Mandela dake ƙauyen Qunu mallakar ta ne.

Ya zuwa yanzu ba tabbas ko Winnie Mandela za ta ɗaukaka kara.