Nijar: Karancin wutar lantarki

A jamhuriyar Nijar jama'a ne ke ta tofa albarkacin bakinsu dangane da matsalar karancin wutar lantarki da ake fama da ita a duk fadin ƙasar.

A ƙasar ta Nijar dai ana fama da karancin wutar lantarki ne masamman a lokacin zafi sabo da tsananin buƙatar wutar.

Kamfanin dillancin wutar lantarki na ƙasar ta Nijar wato NIGELEC na samun wutar ne daga makwabciyar kasar Najeriya.

Tuni dai wasu ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama suka ce, bai kamata ba a duk lokacin da aka fuskanci karancin wutar lantarki kamfanin wutar lantarkin ya rika dora alhakin matsalar akan Najeriya.

Karancin wutar lantarki kusan ya zama ruwan dare a yawancin kasashen Afirka