'Ma'aikatan Nigeria za su daina hawa jirgi mai tsada'

Gwamnatin Najeriya ta ce, daga yanzu ma'aikatan gwamnati za su daina hawa babbar kujerar jirgi ko mai bi mata masu tsada wato First Class ko Middle Class a turance.

Ma'aikatar kudin kasar ta ce irin wadannan tafiye-tafiye a kujerun alfarma na jiragen sama, na janyo wawakeken gibi a kudaden gwamnati da ya kamata a yi wa 'yan kasa aiki da su.

Kakakin ma'akatar kudin Najeriya Festus Akanbi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, kudaden da za a samu daga rage darajar kujerun jiragen saman da maikatan gwamnatin Najeriya ke hawa, za a yi amfani da su wajen yin manyan ayyukan gwamnati don amfanin 'yan kasar.

Kudaden da ake sa ran samu daga rage darajar kujerun jiragen saman sun kai fiye da naira biliyan 18.88.

Ma'aikatar kudin ta kuma ce, za a bukaci ma'aikatan gwamnati da su rika gudanar da taruka a yankunan da suke, sannan kuma dole su nemi izini daga gwamnatin tarayya kafin su shirya wani taro a kasashen waje.