Brussels: An kama mai Malafa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaron Belgium sun tsaurara tsaro a kasar, inda suka kama mutane da dama da suke zargi na da alaka da harin da aka kai a birnin.

Ofishin shigar da kara a Belgium, ya tabbatar da cewa, ana tsare da mutane da dama da ake zargi na da alaka da harin bam din da aka kai birnin Brussels a watan da ya wuce.

Rahotanni da ke fitowa ta kafofin yada labaran kasar na cewa, Mohammed Abrini, dan shekaru 31n da gwamnatin Belgium din dama- ke nema tun watan Nuwamban da ya gabata, gabannin harin da aka kai birnin Paris, na daya daga cikin wadanda aka kama.

Rahotannin na cewa ga dukkan alamu Abrini ne mutumin nan da aka sanya wa suna "Mai Malafa", wanda ake zargi shi ne mutum na uku da bam dinsa ya ki tashi, a harin na Brussels.

Jami'an tsaron sun ce akwai kuma wani da ke tsare mai suna Osama K, wanda ake zargi shi ne aka gani a hoton bidiyo yana magana da daya cikin maharan da suka yi kunar bakin wake a filin jiragen sama na Brussels.