Nigeria: Dalibai sun yi bore kan karanci man fetur

Image caption An rufe jami'ar ne saboda karancin man fetur da ake fama da shi

An rufe jami'ar Lagos da ke kudu maso yammacin Nigeria sakamakon karancin man fetur da ake fama da shi a kasar.

Dalibai sun yi ta bore kan rashin wutar lantarki da ake fama da shi.

Yawan dauke wuta ya zama ruwan dare a Najeriya, don haka jami'o'i da sauran harkokin kasuwanci kan dogara kocokan kan amfani da injinan samar da wuta wato janareto.

Image caption Dalibai sun yi bore kan rashin wuta a jami'ar

Karancin mai ya kuma shafi harkar sufuri, inda dalibai ke shan matukar wahala wajen zuwa jami'ar.

Hukumar jami'ar ta ce za a cigaba da gudanar da harkokin karatu da zarar al'amura sun daidaita.

Karanci man dai za a iya cewa ya zama wani abin kunya ga Najeriya, wadda tana daya daga cikin kasashen da suke da arzikin mai a duniya.