Italiya ta janye jakadan ta daga Masar

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Shugaban Italiya, Sergio Mattarella

Kasar Italiya ta yi wa jakadan ta kiranye daga Cairo, a matsayin rashin amincewa da yadda Masar ta gudanar da bincike kan rasuwar wani dalibin kasar.

An gano gawar dalibin da aka daddatse cikin wani rami a birnin Cairo a watan Fabrairu.

Mista Regeni, wanda ke karatun digirin digirgir a jami'ar Cambridge ta Landan, ya je yin bincike ne kan kungiyoyi da masu fafutuka a Masar.

Wata tattaunawa da aka gudanar a birnin Roma ranar Alhamis, tsakanin masu gudanar da binciken Masar da takwarorinsu na Italiyan bai kammalu ta dadi ba, inda Masar din ta yi watsi da zargin da ke cewa jami'an ta ne suka kashe dalibin.