Fafaroma ya gindaya sabbin dokoki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fafaroma Francis ya ce dokokin ba za su sauya ainihin koyarwar cocin ba
Fafaroma Francis ya fitar da wasu sabbin dokoki ga cocin Katolika kan soyayya da saduwa da kuma aure.

Dokokin wadanda ake kira da Apostolic Exhortation, ba za su sauya tsarin da cocin ke kai ba amma za su bai wa bishop-bishop a duk fadin duniya damar samun 'yancin fassara koyarwar yadda za ta dace da al'adunsu.

Paparoman ya yi kira da a shigar da wadannan dokoki cikin al'amuran cocin a abin da ya kira yanayain da ba kasafai ake samu ba.

An samar da wadannan dokoki ne sakamakon ayyukan da cocin ta gudanar na shekara uku wanda Fafaroman ya jagoranta, inda ya aike da tambayoyi ga mabiya cocin a fadin duniya, da kuma sakamakon tattaunawar da aka yi a tarukan majalisar kirista da aka yi karo biyu.