Za a gina gada ta hade Saudiya da Masar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dangantaka tsakanin Saudiya da Masar tana da kyau kwarai
Sarkin Saudiyya, Salman Ibn AbdulAziz, ya sanar da cewa za a gina gada da za ta tashi daga kasarsa zuwa Masar ta saman Bahar Maliya.

A wata sanarwa da ya fitar, Sarki Salman, ya ce gadar za ta bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar kwana daya Al-Kahira, babban birnin Masar.

Shugaban kasar Masar Abdul-Fattah al-Sisi ya ce, za a sanya wa gadar sunan Sarkin Saudiyya.

Sarkin ya ce, "Ni da dan'uwana al-Sisi mun amince da gina gadar da za ta hade kasashenmu."

Ya kara da cewa, "Wannan wani mataki ne mai cike da tarihi na hada nahiyoyi biyu wato Asiya da Afrika, kuma hakan zai kara karfafa harkokin kasuwanci tsakanin nahiyoyin biyu."

A can baya an sha son gina wannan gadar amma hakan bai yiwu ba.

Kudin da aka kimanta za a kashe wajen gina gadar a baya ya kai kusan dala biliyan uku zuwa hudu, amma ba a fitar da sabon bayani kan kudin da za a kashe a yanzu ba.

Shugaba al-Sisi dai babban abokin gwamnatin Saudiya ne.