An ƙara matsawa kamfanin Apple

Hakkin mallakar hoto Getty

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce, za ta ci gaba neman kamfanin Apple buɗe wata wayar iphone a shari'ar da ta shafi mayagun ƙwayoyi a birnin New York.

Wata wasiƙa da aka gabatarwa wata kotu ta ce, ana ci gaba da buƙatar kamfanin Apple ya tallafa.

Koda a birnin Boston ma wani alƙali ya buƙaci kamfanin Apple ya taimaka a binciken wata shari'a da ake yi.

A baya dai an yi ta sa-in-sa tsakanin hukumar FBI da kamfanin na Apple dangane neman a bude manhajar watar iphone.

Amma a watan Fabrairu wani alkali ya yanke hukuncin cewa, kada a matsawa kamfanin Apple ya bude manhajar wata wayar iphone ta wani da ya aika kisa.