Nigeria za ta nemi tallafin China

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai soma ziyarar yini biyar a China yau Lahadi .

Shugaba Buhari zai tattauna da takwaransa na China Xi Jinping a kan yadda kasar za ta taimakawa Najeriya wajen samar da ababen more rayuwa da suka hada da wutar lantarki da hanyoyi.

Ana kuma sa ran shugabannin biyu za su sa hannu akan yadda zasu bunkasa cinikayya tsakanin ƙasashen.

Haka kuma Shugaba Buhari da Mr Xi za su tattauna akan yadda Chinar za ta taimakawa Najeriya wajen bunkasa fanin aikin noma da ma'adinai.

Tawagar shugaban Nigeria zuwa China za ta haɗa ne da ministoci da wasu gwamnoni.