Sojoji sun kashe 'yan kunar bakin wake 4

Hakkin mallakar hoto

A Najeriya dakarun kasar da ke yaki da 'yan kungiyar Boko Haram sun ce sun samu nasarar hallaka wasu mata 'yan kunar bakin wake.

Su dai matan 'yan kunar bakin waken sun saci hanya ne daga dajin Sambisa za su shiga birnin Maiduguri na jihar Borno da nufin kai hari a jiya Juma'a.

Mukaddashin darekatan yada labarai na rundunar sojin kasa ta kasar Kanar Sani Usman Kukasheka ya ce, sojojin sun yi nasarar harbe uku a kauyen Madiyari, ta hudun kuwa a kauyen Jimini-Bolori, har ma wasu sojinsu sun samu rauni a lamarin.

Ana dai shafe kusan shekaru 6 ana fama da tashin hankalin 'yan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.