Koriya ta arewa ta yi gwajin sabon makami

Koriya ta arewa
Image caption Shugaba Kim Jong-un na Koriya ta arewa

Koriya ta arewa ta ce , cikin nasara tayi gwajin sabon injin na makami mai linzami mai cin dogon zango, wanda kuma ta ce zai bata damar kai wa Amurka hari da makamin nukliya.

Kamfanin dilancin labarai na gwamnati ya ce shugaban kasar, Kim Jong-un da kansa ne ya sa ido akan yadda gwajin ya gudana.

Wannan shi ne shiri na baya baya nan a kokarin da Pyongyang ta ke yi na inganta shirin makamin nukliyarta tun bayan gwajin da ta yi a watan janairun daya gabata.

Matakin ya kuma sa Majalisar dinkin duniya ta sake kakkabawa kasar takunkumi.

Ma'aikatar harkokin waje ta Amurka ta sake yin kira ga Koriya ta arewa a kan ta daina daukar matakan da za su tada zaune tsaye da kuma