Yemen: Za a tsagaita wuta

A Yemen arjejeniyar tsagaita wuta dake samun goyon bayan majalisar ɗinkin duniya za ta soma aiki.

Hakan dai zai kawo ƙarshen yakin da aka shafe shekara guda ana yi, inda aka kashe mutane fiye da 6000.

Tsagaita wutar na zuwa ne gabanin tattaunawar zaman lafiya da za a yi cikin wannan watan tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen Houthi.

Saudi Arabia ce ke jagorantar yakin da ake yi da 'yan tawayen Houthi da ake zargin Iran tana goyon bayansu.

Kafofin yaɗa labarun ƙasar sun bada rahoton zafafar fada tsakanin ɓangarorin biyu gabanin tsagaita wutar.