Chad: Ana zaɓen shugaban ƙasa

Yau take ranar zabe a kasar Chadi, inda wadanda suka cancanta zasu fita rumfunan zabe domin kada kuri'a.

Shugaba mai ci Idris Deby zai fafata da wasu 'yan takarar goma sha uku.

Shi dai Idris Deby yana cikin shugabannin kasashen Afirka da suka jima akan mulki.

Chadi dai kasa ce dake da arzikin mai amma mafi yawan jama'ar kasar suna fama da talauci.