Chadi: Ana jiran sakamakon zaɓe

Hakkin mallakar hoto AFP

A Chadi jama'a suna jiran jin sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi.

Ana dai sa ran shugaba mai ci Idriss Deby zai samu wa'adin mulki na biyar.

Idriss Deby ya kasance yana mulkin Chadi tsawon shekaru 26 tun bayan ya kwace iko ta hanyar juyin mulki.

Jagoran 'yan adawa Saleh Kebzabo ya ce, yana da shaidar gagarumin magudin da aka aikata a lokacin zaɓen.

Gabanin zaɓen dai gwamnati ta ɗau matakan murƙushe masu zanga-zanga da masu nuna adawa da shugaban ƙasar.

Duk da arzikin mai jama'ar Chadi suna rayuwa cikin talauci mai tsanani.