Al Barnawi zai gurfana a gaban kotu

Hukumar tsaro ta farin kaya watau DSS ta ce nan bada jimawa za ta gurfanar da shugaban kungiyar Ansaru Mohammed Usman da aka fi sani da Khalid Al Barnawi gaban kotu.

Ta ce Al Barnawi ɗan ta'ada ne wanda ya riƙa gudanar da ayyukan ta'adanci a Najeriya.

Ana kuma zarginsa da neman matasa da za su shiga ƙungiyoyin ta'adanci irinsu Al Qaeda da ke gabas ta tsakiya da kuma AQIM da ke arewacin nahiyar Afrika.

Hukumar na zargin Al Barnawi da kai hare haren ta'adanci a jihohin Bauchi da Kano da Katsina da Kebbi da kuma Sokoto.

Ta na kuma zargin Al Barnawi da hannu a harin da aka kai wa ofishin Majalisar dinkin duniya da ke Abuja a shekarar 2011, da kuma sace 'yan ƙasashen waje da ke aiki a ƙasar.