Dubai za ta yi gini mafi tsayi

Dubai ta bayyana cewa, za ta yi gini mafi tsayi a duniya, duk da cewa, yanzu haka ma gini mafi tsayi a duniya a Dubai ɗin yake.

Kamfanin da zai yi ginin mai suna Emaar ya ce, sabon dogon ginin zai fi ginin Burj Khalifa tsayi.

Sabon ginin zai kasance da fasali irin na zamani mai juya wasu ɓangarori na ginin.

Kuma ginin zai ƙunshi lambu, da otel-otel da gidaje na ƙasaita.

Sai dai Saudi Arabia ce za ta ciri tutar gini mafi tsayi a duniya wanda ake ginawa a birnin Jeddah.