Kerry ya ziyarci Hiroshima a karon farko

Hakkin mallakar hoto EPA

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya kasance babban jami'in Amurka mafi girman mukami da ya ziyarci Hiroshima tun bayan da Amurka ta jefa makamin kare dangi da ya yi kaca kaca da birnin a 1945.

Mr Kerry ya je birnin na Hiroshima ne domin halartar taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar G7 masu karfin tattalin arziki.

Ana sa ran za su tattauna batutuwa da suka hada da ta'addanci da halin da ake ciki a Gabas Ta Tsakiya da kuma matsalar 'yan gudun hijira.

Haka kuma ana tsammanin Japan za ta yi amfani da abin da ya faru a Hiroshima wajen matsa kaimi ga bukatar rage yawan makaman kare dangi a duniya.

Mr Kerry zai kuma halarci taron addu'oi a gobe Litinin domin tunawa da wadanda suka rasu.

Babu wani shugaban Amurka da ke kan mulki da ya ziyarci birnin.