An yi girgizar kasa a Pakistan

Wata girgizar kasa mai karfi da ta kai maki 6.6 ta auku a kudu maso yammacin Asia inda ta girgiza gine gine a Pakistan da Afghanistan da kuma arewacin India.

Cibiyar binciken yanayin kasa ta Amurka ta ce tsakiyar inda girgizar kasar ta fi karfi yana wani yankin tsaunuka ne tsakanin iyakar Afghanistan da Pakistan kuma zurfinsa a karkashin kasa ya kai kilomita 210.

Haka kuma an jiwo ammon girgizar kasar a Delhi babban birnin kasar India da kewaye.

A dakatar da zirga zirgar jiragen kasa na wani dan lokaci a birnin Delhi.

Babu dai rahotannin hasarar rayuka ko jikkata.