Bakare ya cacccaki gwamnati kan matan Chibok

<span >Babban Faston cocin Latter Rain Assembly da ke Lagos, Fasto Tunde Bakare, ya caccaki gwamnatin Najeriya da gazawa wajen ceto 'yan matan makarantar Chibok 219, wadanda kungiyar Boko Haram ta sace.

Bakare ya bayyana hakan ne a wani taron addu'a na tunawa da shekaru biyu na sace yaran.

Faston ya ce a ganinsa an ja lokaci wajen ceto yaran ne saboda su ba 'ya'yan wane da wane bane.

Ya kara da cewa, "Me kuke tunanin zan yi fiye da wanda nake yi yanzu idan da ace akwai 'yata a ciki? Me ku ke ganin zai faru idan akwai 'yar wani basarake ko shugaban wani coci, ko diyar gwamna ko ta shugaban kasa a ciki?"

Faston ya kuma yabawa kungiyar nan ta masu fafutukar ganin an ceto yaran ta Bring Back Our Girls, inda ya ce ta fita zakka wajen kokarin da take na ganin yaran sun dawo gaban iyayensu.

Fasto Bakare ya kara caccakar gwamnati da jam'iyyun siyasa kan yadda suka sanya siyasa kan batun sace yaran.

Ya kuma kara nuna damuwa kan cewa lallai ya kamata a kara zage dantse wajen neman sanin inda yaran suke don ceto su.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne 'yan matan makarantar Chibok za su cika shekaru biyu cif da sace su da mayakan Boko Haram suka yi daga makarantarsu.