Human Rights Watch ta bukaci hukumomi su tsare makarantu".

Tambarin kungiyar Human Rights Watch Hakkin mallakar hoto website
Image caption Tambarin kungiyar Human Rights Watch

ƙungiyar Human Rights Watch ta ce hare-haren Boko Haram a makarantu sun yi mummunan tasiri kan ilimin boko a arewa maso gabashin Najeriya.

A wani rahoto da ta fitar ƙungiyar ta kare hakkin biladaman ta kuma ce ƙungiyar ta Boko Haram ta lalata makarantu sama da ɗari tara sannan ta tilasata rufe makarantu aƙalla dubu da ɗari biyar tsakanin shekarun 2009 da 2015.

Rahoton ƙungiyar ya ce yara kusan miliyan daya ne rikicin Boko Haram ya haramta wa damar samun ilimi a yankin.

Sai dai kuma ya ce dakarun Najeriya ma suna da laifi wajen hana yara karatu saboda maida wasu makarantu sansanoni da suka yi.

Kana ya ce an kashe malaman makaranta ɗari da goma sha daya, tare da tliastawa dubu goma sha tara tserewa.

Ga karin bayani a rahoton da wakilinmu Muhammad Kabir Muhammad ya hada mana.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti