Kasafin 2016: Takaddama tsakanin 'yan majalisa da gwamnati

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yakubu Dogara ya karyata rahotannin jaridu kan wannan batu
Wata sabuwar takaddamar ta kunno kai tsakanin majalisar dokokin Nigeria da bangaren gwamnati kan zargin cire kwangilar shimfida layin dogo daga Lagos zuwa Calabar, daga cikin kassafin kudin 2016.

Wasu majiyoyin gwamnatin kasar sun ce an kebe Naira biliyan 60 domin wannan aikin a cikin kudirin kasafin kudin da shugaban kasar ya mika wa majalisar bayan yin gyare-gyare, amma sai 'yan majalisar suka soke aikin tare da karkata kudaden zuwa ga wasu fannoni.

Za a iya cewa dai wannan batun shi ne ya kankane shafukan twitter a kasar ta Najeriya a duk tsawon ranar Lahadi.

Shugaban kwamitin kassafin kudi na majalisar wakillai Hon. Abdulmumini Jibril ya bayyana ta wani gidan talbijin cewa babu wani abu kamar kwangilar shimfida layin dogo daga Lagos Zuwa Calabar a cikin kudurin kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar.

Tun da fari dai jaridun kasar ne da dama suka buga a karshen mako inda suka zargi 'yan majalisar da cire wannan kwagilar ta Naira biliyan 60 daga kasafin, zargin da kakakin majalisar wakilan da kansa ya karyata.