Daily Mail na cinikin kamfanin Yahoo

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kakakin jaridar Daily Mail ya furta cewa kamfanin dillancin labarai na AP shi ya soma tattaunawa kan maganar tun da farko.

To sai dai ga dukkan alamu babu tabbacin ko kamfanin Daily Mail zai iya harkar.

Jaridar Wallstreet Journal tun a baya ta ruwaito cewa Daily Mail da General Trust na cikin tattaunawa da wasu kamfanoni masu zaman kasansu game da cinikin.

Kamfanin na Yahoo dai na cikin wani yanayin irin na tsaka mai wuya.