Intanet ya dauke a Chadi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Idris Deby ya sake tsayawa takarar karo na biyar
Hanyar sadarwa ta Intanet ta dauke a Ndjamena babban birnin Chadi, kwana guda bayan da aka yi zaben shugaban kasa.

Hanyar sadarwa ta intanet a wayoyin hannu ta dauke tun safiyar Lahadi, yayin da intanet din ya dauke kocokam har a sauran hanyoyin sadarwar ma da yamma.

Kazalika ba a iya aikawa da sakon kar ta kwana a wayoyin hannu.

Daukewar sadarwar wadda, ba a samu wani bayani a hukumance ba a kanta, na hana tattaunawa tsakanin jama'a kan yadda zaben kasar ya gudana.

Har yanzu dai sakamako bai kammala ba, inda aka fafata tsakanin 'yan takara 12 har da shugaba Idris Deby wanda ya shafe shekaru 26 yana mulkin kasar.