Nigeria: An kulle ofishin hukumar NFF

Image caption Motar yan sanda a bakin ofishin hukumar ta NFF

Jami'an tsaro sun yi wa ofishin hukumar ƙwallon ƙafar Najeriya wato NFF, ranar Litinin.

Hakan dai ya biyo bayan hukuncin da wata kotu a birnin Jos da ke jihar Filato, ta yanke na korar shugabancin hukumar karkashin jagorancin Amaju Pinnick, ta kuma nemi da Chris Giwa ya zama sabon shugaban hukumar.

A watan Satumban 2014 ne dai aka yi zaben hukumar, a inda Amaju Pinnick ya samu nasara bisa abokin takararsa, Chris Giwa.

Bangaren Chris Giwa sun ce rufe ofishin yana da nasaba da gudun ka da bangaren Amaju Pinnick sun canza alkaluma na almundahanar da suka yi.

Sai dai kuma Sakatare Janar na bangaren Amaju Pinnick, Dr Muhammad Sunusi, ya shaidawa BBC cewa shi yana cikin ofishin domin gudanar da ayyukansa na yau da kullum.

Ya ce kara da cewa babu inda za su har sai sun samu takarda daga kotu.