Shugaba Buhari ya fara ziyara a China

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya soma ziyarar aiki a China, inda zai gana da takwaran aikinsa na China Xi Jinping.

Hukumomin Najeriya dai sun ce manufar ziyarar ita ce karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu a yunkurin gwamnatin ƙasar na fadada hanyoyin samun kuɗin shiga, da bunƙasa harkar noma, da hakar ma'adinai.

Sun kuma ƙara da cewa shugabannin ƙasashen biyu za su kammala cimma wasu yarjejeniyoyi da dama da suka danganci habaka cinikayya, da karfafa dankon zumunci ta fuskar tattalin arziki.

Sai dai kuma abin da ya fi jan hankalin wasu 'yan Najeriya game da ziyarar shi ne batun karbo bashi don cike giɓin kasafin kuɗin asar na bana.

Mr Femi Falana wani lauya ne mai zaman kansa, kuma mai fafutuka a Najeriyar, ya rubuta wa ministar kuɗi ta ƙasar wasiƙa yana jan kunnen gwamnatin kada ta kuskura ta karɓo bashi.

Ga kuma hirar da yayi da wakilinmu Muhammad Kabir Muhammad.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti