An afkawa jirgin ruwan Turkiyya a Najeriya

Image caption Masu fashin tekun Somaliya sun ragu sakamakon tsananta tsaro a bakin tekun gabashin Afrika.

Rahotanni daga kafofin yada labarai a Turkiyya na cewa masu fashin teku a gabar tekun Najeriya sun kai wa wani jirgin ruwan daukar kaya na Turkiyan hari, inda suka yi garkuwa da mutane shida.

Kamfanin dillancin labarai na Deniz ya ce masu fashin tekun sun sace da injiniyan jirgin ruwan da mai gyaran wutar lantarki da mai bayyana taswira, da kuma uku daga cikin matuka jirgin ne a wani yanki da ake fama da fashin teku.

Jirgin mallakin kamfani Kaptanogul Shipping ne, wanda ya ce wadanda aka yi garkuwa da su da ma sauran da suka rage kan jirgin na cikin koshin lafiya.

Ba a tabbatar da yawan mutanen da ke cikin jirgin na M/T Puli wanda ke dauke da sinadarai a lokacin da aka afka masu ba.

Jami'an kamfanin sun ce ya zuwa yanzu dai masu fashin basu kira su ba tukun.

Yawan fashin da ake fama da shi a tekun Somalia da ke gabashin Afrika ya ragu a shekaru uku da suka gabata, ganin yadda aka tsananta tsaro da kuma jiragen yakin da aka kafa na jami'an tsaro daga kasashen waje.