Rasha: Dan kunar bakin wake ya tayar da bam

Hakkin mallakar hoto SYRIA REBELS GATHERING
Image caption Babu wanda ya mutu a harin baya ga dan kunar bakin waken
'Yan sanda a Rasha sun ce wani dan kunar bakin wake ya kai hari wani ofishinsu da ke yankin Stavropol a kudancin kasar.

Dan kunar bakin waken ya mutu sakamakon tashin bam din a jikinsa, kuma 'yan sanda sun kashe sauran maharan biyu.

Babu dai wanda ya mutu ko ya samu rauni sakamakon harin, baya ga adan kunar bakin waken.

Ofishin 'yan sandan da aka kai wa harin dai na gundunar Novoselitskoye ne a yankin V,, kusan nisan kilomita 150 daga gabashin Stavropol.