Rarara ya sha da kyar

Hakkin mallakar hoto Rarara
Image caption Rarara shahararren mawakin siyasa ne
Wasu 'yan bindiga sun kwace a kalla naira miliyan 2.8 da kuma mota wadda kudinta zai kai naira miliyan tara daga hannun mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara.

A ranar Alhamis da dare ne mutanen suka tare shi a unguwar Tudun Fulani, suka kai shi wani waje, inda suka ce masa an aiko su su kashe shi ne, amma yana iya fansar kansa da kudi.

Wani aminin Rarara kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma'ila Na'abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa a lokacin Rarara na da wasu kudade a motarsa wadanda ya fitar da su daga banki a ranar domin zuwa garinsu a washegari don gudanar da wani aiki.

Ya kara da cewa mutanen sun mammare shi suka kuma dora masa bakin bindiga aka don kada ya yi musu.

Daga karshe sun kyale shi a wajen da misalin karfe uku na tsakar dare ba tare da wani taimako ba suka gudu da abubuwan da suka kwace. ukumar 'yan sanda na ci gaba da binciken faruwar al'amarin.