Blackberry zai kaddamar da sabbin wayoyi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Blackberry ya fuskanci cikas na kimanin dala miliyan 200 wajen sayar da wayoyin sa a cikin watanni uku

Kamfanin Blackberry zai kaddamar da wasu sabbin wayoyin ko mai da ruwan ka har guda biyu a wannan shekarar.

Shugaban kamfanin John Chen shi ne ya sanar da hakan.

Ya ce za'a sanyawa daya daga cikin wayar wurin latsawa don sarrafa wayar yayin daya kuma za'a rika shafawa don sarrafa wayar ta komai da ruwanka.

Kamfanin dai ya fuskanci cikas na kimanin dala miliyan 200 wajen sayar da wayoyin sa a cikin watanni uku na baya bayan nan daya kare a watan Fabrairu.

A watan daya gabata ne shafin sada zumunta da muhawara na Facebook da kuma Whatsapp na aikewa da sakonni suka ce za su dakatar da taimakon da suke bai wa manhajar Blackberry da ke shafuffukan su.