Brazil: Rouseff na kara fuskantar matsin lamba

Hakkin mallakar hoto AP

Jam'iyyar kawance ta PP ta fice daga gwamnatin Brazil, tare matsin lamba kan shugaba gabanin kada kuri'ar tsige ta a ranar Lahadi.

Jam'iyyar ta Progressive Party (PP) wacce ita ce ta huɗu kuma mafi girma a cikin gwamnatin ƙasar, ta ce akasarin mambobin majalisarta ne za su kada ƙuri'ar tsige Ms Rousseff .

Amma kuma babu tabbaci ko ficewarta daga gwamnati zai shafi ƙuri'un da za a kaɗa ranar Lahadi.

A watan da ya gabata ne jam'iyyar PMDB wacce ita ce mafi girma a cikin gwamnatin haɗakar ta Brazil ta kaɗa kuri'ar ficewa.

Ms Rousseff, wacce ke fuskantar tsigewa ta ce yan adawa ne ke son kifar da gwamnatin ta.

Ana zarginta ne badaƙalar cin hanci da almundahana da kuɗaɗen gwamnati gabanin yakin neman zabenta shekaru biyu da suka gabata.