HTC ya samfurta kyamarar wayarsa ta HTC 10

Hakkin mallakar hoto AFP

Kamfanin HTC ya sanar da samfurin wayar komai-da-ruwanka mai kyamarar dauki-da-kan-ka, da aka zayyana don magance hotuna masu dishi-dishi.

HTC din ya kirkiri wanann kyamara da siffar mudubi mai amfani da fasahar iya saita hoton da zai fita da kyau ko da kuwa hannu na rawa.

Wannan shine karon farko da aka samu wanann siffar mudubi a kyamarar gaba ta wayar salular samfurin HTC 10.

Kamfanin ya kuma ce kyamarar baya ta wayar HTC 10 ita ce ta daya a cikin kyamarorin wayoyin komai da ruwan ka.

Sai dai masu sharhi na shakku kan ko kirkirar irin wadannan siffofi na kyamara sun wadatar wajen kara wa kamfanin HTC din na kasar Taiwan tagomashi.