Za a yi wa harkar shirya fina-finai garanbawul

Hakkin mallakar hoto Lai Mohammed Facebook
Image caption Ministan yada labarai Lai Mohammed ya ce za ana so harkar fina-finai ta habaka a Najeriya
Ministan yada labarai na Nigeria Alhaji Lai Mohammed, ya kaddamar da wani kwamiti na majalisar shirya fina-finai na kasar MOPICON a ranar Talata.

Ya kaddamar da kwamitin ne a wani kokari na ganin an gabatar da kudurin doka na MOPICON da gaggawa.

Da yake kaddamar da kwamitin a birnin Lagos, Alhaji Mohammed ya karyata jita-jitar cewa gwamnati ta samar da hukumar ne domin samun damar sarrafata yadda ta so.

Ministan ya ce kokarin gwamnati shi ne domin bai wa fagen shirya fina-finai na Najeriya damar taka rawarsu wajen cigaban kasa.

Ya kara da cewa hakkin ma'aikatarsa ne ta sa ido kan harkar fina-finai da kuma yadda za a tallafawa bangaren.

A karshe ya bai wa kwamitin wanda ya hada da wakilan kungiyoyi daban-daban da hukumar tace fina-finai ta kasa makonni uku su kammala aikin da ya basu tare da mika masa rahoto.