Shugaban Niger ya nada sabbin Ministoci

Hakkin mallakar hoto
Image caption A watan da ya gabata ne Muhammadou Issoufou ya lashe zaben kasar

Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issoufou ya nada sabuwar gwamnatinsa mai mambobi 38 karkashin jagorancin Firai minista Briji Rafini.

Wasu daga cikin manya manyan kalubalan da ke gaban majalisar ministocin nasa dai sun hada da hada kawunan 'yan kasar, da yin aiki tukuru domin habaka tattalin arziki da kyautata jin dadin rayuwar 'yan kasa.

Sai dai wasu kungiyoyin farar hula da ma talakawa na ganin adadin ministocin ya yi yawa idan aka yi la'akari da cewa Nijar kasa ce mai raunin tattalin arziki.

Ga rahoton da Baro Arzika ya aiko mana daga Nijar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A watan da ya gabata ne Muhammadou Issoufou ya lashe zaben shugabancin kasar a karo na biyu.