An gano ma'aikatan bogi a jihar Kano

Image caption Gwamnatin jihar tace yanzu zata rika samun rarar sama da naira miliyan 280

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya tace ta gano ma'aikatan bogi sama da dubu bakwai a cikin ma'aikatan jihar.

Gwamnatin jihar tace gano mutanen da aka yi zai sa gwamnatin samun rarar sama da naira miliyan 280.

An dai gano mutanen ne sakamakon tantance ma'aikatan jihar da ake ci gaba da yi a halin yanzu.

Shugaban ma'aikatan na Kano Alh. Muhamadu Na Iya ya shaida wa BBC cewa gwamnati zata ci gaba da sa ido sosai kan ma'aikatar tare da daukar matakai na kyautata jin dadin ma'aikatan jihar.