Yawan yaran da ke ƙunar baƙin wake ya karu — MDD

Hakkin mallakar hoto

Majalisar Dinkin Duniya ta ce amfani da yara a matsayin 'yan ƙunar baƙin wake da ƙungiyar Boko Haram take yi ya ninka sau 11 a cikin shekara ɗaya.

Asusun tallafawa ƙananan yara na Majalisar, UNICEF ya ce an yi amfani da yara 44 domin yin ƙunar baƙin wake a ƙasar Kamaru da Chadi da kuma Najeriya a shekara daya da ta wuce, idan aka kwatanta da 'yan ƙunar baƙin wake hudu a shekarar 2014.

Majaliasar Dinkin Duniya ta ce a yanzu ɗaya a cikin 'yan ƙunar baƙin wake biyar yara ne, uku cikin hudu kuma yara mata ne.

UNICEF ya ce a mafi yawancin lokuta ana bai wa yaran kwaya ne, sai a daura musu bam a jikinsu kuma a tursasa musu su kai hari.

Rikicin na Boko Haram wanda ya fi shafar arewa-maso-gabashin Najeriya da kuma makwabtanta da ke kusa da tafin Chadi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 17000.

Asusun tallafawa ƙananan yaran ya ce an tursasa wa ƙananan yara miliyan 1.3 barin gidajensu a ƙasashe hudu wadanda suka hada da Kamaru da Chad da Najeriya da kuma Nijar.