Me ya kamata ka sani kan Yemen?

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Akalla kashi 80 cikin dari na al'ummar Yemen na dogara ne da daukin abinci da ake kai masu. Wanna hoton ya nuno 'yan kasar sun yawo a kasuwar birnin Sanaa ranar 9 Afrilu 2016.

Yarjejeniyar tsagaita wutar da ta soma aiki ranar Litinin a Yemen za ta kawo karshen tarzomar da kasar ta shekara tana fama da ita.

Yarjejeniyar na zuwa ne kafin tattaunawar zaman lafiya da za a gudanar mako mai zuwa a Kuwait.

BBC ta duba abubuwa biyar da ya kamata ka sani game da Yemen.

1. Dama can Yemen na daya daga cikin kasashen Larabawa da suka fi fama da talauci, ganin yadda rijiyoyin man nasu suka soma bushewa. Tunda tarzomar ta fara a bara, aka rushe duk gine-gine a kasar, kuma tattalin arzikin ya shiga halin ha'ula'i, kazalika a kalla kashi 80 cikin 100 na al'ummar kasar da suka kai kimanin miliyan 26 na dogara ne da daukin abinci da ake kai musu.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Tsohon shugaban kasar Yemen ne ke goyon bayan 'yan tawayen Houthi. Wannan hoton ya nuna masu goyon bayan Houthi dauke da makaran wani cikin mayakan da aka kashe a yakin da suke yi da dakarun hadin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta a birnin Sanaa ranar 10 Afrilu 2016.

2. Sama da mutane dubu 6 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar rikice-rikice tsakanin mayakan Houthi da magoya bayan gwamnatin Yemen. Fiye da mutane miliyan 2.5 ne kuma suka rasa muhallansu.

3. Yemen ta rabu kashi-kashi, da 'yan tawayen Houthi da magoya bayan shugaba mai mulki da dakarun sojin yankuna Larabawa da kuma masu ikirarin jihadi daga kungiyoyin Al-Qaeda da IS. 'Yan tawayen sun zargi gwamnatin da cin hanci da rashawa da kuma shirin mayar da su saniyar ware ta hanyar amfani da tsarin birnin tarayya.

4. 'Yan Houthi- watau 'yan tawaye Musulmai mambiya shi'a -- suna samun taimako daga jami'an da ke goyon bayan tsohon shugaban kasar, wanda aka tilastawa gudun hijira a watan Maris din shekarar 2015. Hadin gwiwar dakarun soji da Saudiyya ke jagoranta sun soma luguden wuta a watan Maris din baran, inda suke fatan karya lagon 'yan tawayen Houthin da suka mamaye rabin kasar. Jami'an tsaro da ke goyon bayan gwamnati da kuma mayakan da ke kudancin kasar, suna samun taimako daga jami'an hadin gwiwar kasashen da Saudiyya ke jagoranta, inda har suka samu kwato yankuna biyar a kudancin kasar.

5. Wasu na ganin tarzomar Yemen kamar yakin kananan kungiyoyi da ke tsakanin yankuna biyu a Gabas Ta Tsakiya: Watau Saudiyya da Iran. Mabiya Sunna sun fi rinjaye a Saudiyya, inda har 'yan shi'a da basu da yawa a kasar ke korafin cewa an mayar da su saniyar ware. A Iran kuma 'yan Shi'a ke da rinjaye a kasar. Sassan biyu na fafutukar neman rinjaye a taswirar Gabas Ta Tsakiya da ke sauyawa a kullum.