Yan fansho a Bauchi na cikin ukuba- NLC

Hakkin mallakar hoto Bauchi State Govt
Image caption Gwamnatin jihar Bauchi ta ce duk wanda aka tantance shi zai samu albashinsa a kan kari

A jihar Bauchi dake arewacin Nijeriya, ma'aikatan gwamnati da 'yan fansho na ci gaba da nuna damuwa kan halin da su ke ciki inda wasunsu suka kwashe watanni hudu babu albashi, yayin da gwamnatin ke aikin tantance su da nufin fitar da na bogi.

A baya dai gwamnatin jihar ta bayyana cewa an samu ma'aikatan bogi kimanin dubu 22 a jihar, amma daga bisani aka gano cewa akwai kura-kurai a alkalumman saboda sun haɗa har da dimbin ma'aikata na hakika lamarin da ya tilasta yanzu gwamnati ke sake aikin tantancewar.

Gwamnatin dai ta ce duk wanda aka tantance shi zai samu albashinsa a kan kari, amma wasu ma'aikata da aka tantance na cewa har yanzu lamarin ya faskara kana wasunsu na cewa shugabannin kungiyoyin kwadago a jihar basa hubbasan a zo a gani.

Shugaban hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, reshen jihar Bauchi, Comrade Hashimu Muhammad Gitel ya shaida wa BBC cewa ma'aikatan na cikin mawuyacin hali kuma kungiyar na ci gaba da fafutikar ganin gwamnatin jihar ta biya su hakkokinsu.