Nigeria: Dogara zai gana da Buhari

Image caption Tun lokacin da shugaba Buhari ya mika kasafi ga majalisa, ake ta musayar yawu

Kakakin majalisar wakilai ta Najeriya, Yakubu Dogara zai gana da shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari game da ja'in-ja kan kasafin ƙasar.

Majalisar Wakilan ce dai ta buƙaci kakakin nata, Yakubu Dogara, da ya tuntubi fadar shugaban ƙasa don jin hakikanin matsalolin da ɓangaren zartarwa ya hango a kasafin kuɗin ƙasar na bana.

Hakan ya biyo bayan zargin da ake yi wa 'yan majalisun na yi wa gwamnatin Buhari cikas, sakamakon yin fatali da ginin layin dogo daga birnin Legas zuwa Kalabar na jihar Cross River, daga kasafin kudin.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Abdulrazak Namdas, ya shaidawa BBC cewa sun ki amincewa da batun layin Dogon ne saboda ba shugaban ƙasa ne ya kawo musu ba.

An dai ce ministan sufuri, Rotimi Amaechi ne ya mikawa 'yan majalisar buƙatar ginin layin dogon, abin da suka ce hakan ya saɓa dokokin majalisar.