Masu zamba ta intanet suna haƙon iPhone

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Masu zambar dai suna amfani ne da irin amannar da masu wayoyin iPhone suka yi da kamfanin Apple wajen kare musu sirri

Masu zamba ta intanet suna haƙon masu amfani da kayan kamfanin Apple saboda tunanin za a iya sanin kuɗaɗen da suke samu, kamar yadda wani masanin harkar tsaro ya yi gargaɗi.

Wani marubucin intanet, Graham Cluley ya ce manhajojin da ake amfani wajen zamba sun fi yawa a manhajar Windows.

A ranar Litinin, mista Graham ya kai koke kan wani saƙon wayar tafi da gidanka na zamba da ake ƙoƙarin yaudarar mutane domin neman bayanansu na sirri.

Sai dai kuma shafin ɓangaren kula da abokan hulɗar kamfanin Apple ya gargaɗi abokan hulɗarsu da su guji shiga irin waɗannan shafukan na zamba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mazambatan suna aike da sako cewa lambobin sirrin wayar za su daina amfani

Mazambatan dai suna aike da saƙo zuwa wayoyin mutanen cewa lambobin sirrinsu na wayar Apple za su daina aiki.

Saƙon yana neman mutanen su ziyarci wani shafin intanet na jabu, a inda za a umarce su da su shigar da bayanansu na sirri.

Mista Cluley ya ce " saƙon yana son samun bayanan masu amfani da wayoyin da kuma bayanan da ke ɗauke a katinansu na saye da sayarwa."

Ya ƙara da cewa " mazambatan suna amfani da irin imanin da masu amfani da wayoyin Apple suka yi cewa kamfanin ba zai zambace su ba."