Buhari ka ceto 'yan Chibok — Malala

Image caption Malala dai ta taba zuwa Najeriya domin taya iyayen 'yan matan Chibok alhini

Yarinyar nan mai fafutuka 'yar ƙasar Pakistan Malala Yousufzei ta yi kira ga shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari da cewa ka da ya gajiye wajen kokarin ganin ya ceto 'yan matan Chibok.

Malala ta yi wannan kira ne a wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta aikowa iyayen yaran makarantar Chibok ɗin da kungiyar Boko Haram ta sace shekaru biyu da suka gabata, domin taya su jimami.

Ta ce: "Shin shugaba zai iya hakura da cigaba da neman 'ya'yansa kuwa? To ina kira ga shugaba Buhari kamar yadda na yi a bara cewa ya ƙara zage dantse wajen ganin an kubutar da yaran nan."

Malala ta kuma ce a wannan lokaci da 'yan matan ke cika shekaru biyu ba tare da jin ɗuriyarsu ba, ya zama wajibi ta taya iyayensu alhini da kuma fatan su ga 'ya'yansu nan gaba har ma su rungume su.

"Fatana Allah yasa wata rana su dawo gida su kammala karatunsu su kuma samu kyakkyawar rayuwa," In ji Malala.

Ta ƙara da cewa yanzu lokaci ya yi da ya kamata kowa ya sa hannu wajen ganin an gano inda 'yan matan suke da kuma ceto su.