Kasashen Afrika na fama da fari

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban Malawi, Peter Mutharika ya bayyana matsalar karancin abincin da kasar ke fama da ita a matsayin bala'in da ya shafi kasa baki daya.

Shugaba Mutharika, ya ce wasu jama'ar kasar za su bukaci agajin abinci har na tsawon shekara daya. Mozambique da Zimbabwe ma na fuskantar matsalar ta karancin abinci.

Yawancin kasashen da ke kudancin nahiyar Afrika na fama da matsalar karancin abincin, sakamakon fari da ambaliyar ruwa.

Gwamnatin Mozambique ta sanar da cewa ana fama da mummunan fari a kudanci da yankuna da ke tsakiyar Afrika.

A kasar Zimbabwe kuma, fiye da kashi daya cikin hudu na mutanen kasar ba su da isasshen abinci.

Afrika Ta Kudu kuma ta ce wannan fari na bana ya fi na duk sauran shekaru muni.