Buhari ya gana da Firai ministan China

Hakkin mallakar hoto Garba Shehu
Image caption Rahotanni na cewa bashin zai taimakawa Nigeria kwarai

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya yi wata tattaunawa da Firai ministan China Li Keqiang , yayin ziyarar da yake yi a ƙasar.

Sun yi ganawar ne bayan da China ta sanar da bai wa Najeriya bashin dala miliyan shida domin samar da abubuwan more rayuwa.

Sai dai jami'an Najeriya sun ce za su gabatar wa China irin ayyukan da za a yi da kuɗin.

Samun wannan bashi dai na nuna cewa makasudin ziyarar shugaba Buharin ta yi tasiri.

Gwamnatin Najeriya na son ƙara yawan kuɗaden da ake kashewa wajen samar da kayayyakin more rayuwa, amma kuma ana samun cikas dangane da hakan saboda raguwar kuɗin shigar ƙasar, sakamakon faɗuwar farashin man fetur a duniya.

China ta sanar da bayar da bashin ne a daidai lokacin da asusun bayar da lamuni na duniya IMF, ya yi gargadi cewar bunƙasar tattalin arzikin Najeriya zai yi ƙasa a bana.