Saudiya za ta rage karfin Askar

Image caption 'Yan hisban Saudi na wuce ka'ida wajen hukunci

<span >Saudiyya zata shigo da sabbin dokoki domin rage karfin 'yan sandan hisba na kasar, wadanda a 'yan shekarun bayan nan ke shan suka kan amfani da karfinsu ba bisa ka'ida ba.

Sabuwar dokar zata hana 'yan sandan hisban bin sahun mutane tare da kamasu, ko kuma neman su nuna takardun shaidarsu.

Dokokin wadanda majalisar zartarwar kasar ta amince da su--- sun nemi 'yan sandan hisban da kada su dauki doka a hannunsu idan suka ga an keta tsauraran dokokin addini a kasar.

A maimakon hakan an bukaci su kai rahoton ga rundunar 'yan sandan kasar wadanda za su dauki kowane irin mataki da ya dace kan mutanan da ake zargi.