Sabuwar fasahar gina gida cikin sauki

Fasahar gina gida Hakkin mallakar hoto Space Craft SystemsWikiHouse NZ
Image caption Fasahar gina gida

Sabuwar fasahar da za a iya maida gida tamkar na komai da ruwanka za ta iya yin tasiri ne idan kana da irin tsarin ginin da kake so tun da farko.

Akasari a wajen mutane gidajen komai da ruwanka ba wai wanda ke da na'urar mai amfani da bukatun yanayin zafi ko sanyi ba, ko kuma na'urar sanyaya abinci wato firjin, da ya san lokacin da madarar da ke cikinsa ta kare, a maimakon haka wuri ne da ya kasance mai dadin zama, da kuma kyau , kana a wurin da ya dace.

Amma kuma abin takaici shine, wasu har yanzu na ganin hakan tamkar wani mafarki ne mai kuma nisa da zama gaskiya-- suna diga ayar tambaya cewa, shin akwai wata fasahar da za ta iya taka rawa wajen samar wa da mutane gidaje cikin sauki da kuma irin wanda zai yi daidai da bukatunsu?

Alaister Parvin na tunanin hakan zai yiwu, shine kashin bayan ginin WikiHouse, wani gini mai budadden tsari da ke nufin bai wa mutane kayyakin aikin da zasu iya gina gidaje masu sauki.