Amurka za ta ba da $240 miliyan don farfado da tafkin Chadi

Image caption Yankin tafkin Chadi ya hada da kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi

Amurka ta ce za ta bayar da fiye da dala miliyan 240 domin taimaka wa ayyukan jin kai a yankin tafkin Chadi.

Amurkan ta sanar da wannan batu ne a wata sanarwa da ofishin jakadancinta da ke Najeriya ya fitar don nuna alhininta kan cika shekara biyu da sace 'yan matan makarantar Chibok da har yanzu ba labarinsu.

Ta ce za a yi amfani da kudin ne domin taimaka wa mutanen da yakin kungiyar Boko Haram ya tarwatsa wajen daidaita tunaninsu da inganta harkar lafiyarsu da bayar da agajin gaggawa da ilimin yaransu wadanda yakin ya raba da gidajensu.

Sanarwar ta kuma yi kira ga kungiyar Boko Haram da ta gaggauta sakin 'yan matan Chibok da dukkan wadansu mutane da ta sace ba tare da sanya wasu sharudda ba.